Irmiya3hau_bib
1“In mutum ya saki matarsata kuwa bar shi ta auri wani mutum,zai iya komo da ita kuma?Ƙasar ba za tă ƙazantu gaba ɗaya ba?Amma kun yi rayuwa kamar karuwa da masoya masu yawayanzu za ki komo wurina?”In ji Ubangiji.2“Ta da idanu ki duba tsaunuka ki gani.Akwai wani wurin da ba a kwana da ke ba?A gefen hanya kin zauna kina jiran masoyanki,kin zauna kamar makiyayi a hamada.Kin ƙazantar da ƙasarda karuwancinki da muguntarki.3Saboda haka an hana yayyafi,kuma babu ruwan bazara da ya sauka.Duk da haka kina da irin kallon da karuwa takan yi;kin ƙi ki ji kunya.4Yanzu ba kin kira ni,‘Mahaifina, abokina daga ƙuruciyata ba,5kullum za ka riƙa fushi?Hasalarka za tă ci gaba har abada ne?’Haka kike magana,amma kina aikata dukan muguntar da kika iya yi.”