1Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,2“Tafi ka yi shela a kunnuwar Urushalima cewa,“ ‘Na tuna da amincin ƙuruciyarki,yadda kamar amarya kika ƙaunace nikika kuma bi ni cikin hamada,cikin ƙasar da ba a yi shuka ba.3Isra’ila tsattsarka ce ga Ubangiji,nunan fari na girbinsa;dukan waɗanda suka cinye ta an same su da laifi,masifa kuwa ta same su,’ ”in ji Ubangiji.4Ka saurari maganar Ubangiji, ya gidan Yaƙub,dukanku zuriyar gidan Isra’ila.5Ga abin da Ubangiji yana cewa,“Wane laifi ne kakanninku sun same ni da shi,da suka tsaya nesa da ni?Sun bi gumakan banzasu kansu suka kuma zama banza da kansu.6Ba su yi tambaya, ‘Ina Ubangiji,wanda ya fitar da su daga Masarya bishe su cikin jejicikin hamada da kwazazzabaiƙasa mai fări da kuma duhu,ƙasar da ba kowa mai ratsa ta ba kowa kuma mai zama a cikinta?’7Na kawo ku zuwa ƙasa mai albarkadon ku ci amfaninta da abubuwa masu yalwar da take bayarwa.Amma kuka zo kuka ƙazantar da ƙasatakuka kuma mai da gādona abin ƙyama.8Firistoci ba su yi tambaya,‘Ina Ubangiji ba.’Waɗanda suke amfani da doka ba su san ni ba;shugabanni suka yi mini tawaye.Annabawa suka yi annabci ta wurin Ba’al,suna bin gumakan banza.9“Saboda haka ina sāke tuhumarku,”in ji Ubangiji.“Zan kuma tuhumi ’ya’ya ’ya’yanku.10Ku ƙetare zuwa tsibiran Kittim ku gani,ku aika zuwa Kedar ku duba da kyau;ku ga ko an taɓa yin wani abu haka.11Akwai wata al’ummar da ta canja allolinta?(Duk da haka su ba alloli ba ne sam.)Amma mutanena sun musayar da ɗaukakarsuda gumakan banza.12Ku girgiza saboda wannan, ya sammai,ku kuma razana don tsoro mai girma,”in ji Ubangiji.13“Mutanena sun aikata zunubai guda biyu.Sun rabu da ni,ni da nake maɓulɓular ruwan rai,sun kuma haƙa tankunan ruwansu,tankuna ruwan da suka fashe da ba za su iya riƙe ruwa ba.14Isra’ila bawa ne, bawa ne ta wurin haihuwa?Me ya sa ya zama ganima?15Zakoki sun yi ruri;sun yi masa ruri.Sun lalatar da ƙasarsa;an ƙone garuruwansa aka kuma watse daga ciki.16Haka ma, mutanen Memfis da Tafanessun aske rawanin kanka17Ba kai ne ba ka jawo wa kanka bata wurin rabuwa da Ubangiji Allahnkasa’ad da ya bi da kai a hanya?18To, me ya sa za ka Masardon shan ruwa daga Shihor?Kuma me ya sa za ka Assuriyadon shan ruwa daga Kogi?19Muguntarka za tă hukunta ka;jan bayanka zai tsawata maka.Sai ka lura ka kuma ganeyaya mugu da kuma ɗaci suke a gare kasa’ad da ka rabu da Ubangiji Allahnkakuma ba ka tsorona,”in ji Ubangiji Maɗaukaki.20“Tun da daɗewa ka karya karkiyarkaka kuma tsintsinke sarƙoƙinka;sai ka ce, ‘Ba zan bauta maka ba!’Tabbatacce, a kan kowane tudu mai tsayida kuma a ƙarƙashin kowane ɗanyen itaceka kwanta kamar karuwa.21Na shuka ka kamar zaɓaɓɓen inabiiri mai kyau da kuma wanda za a dogara a kai.Yaya kuma ka juya kana gāba da nika lalace, ka zama inabin jeji?22Ko da yake ka wanke kanka da sabuluka yi amfani da sabulu mai yawa,duk da haka har yanzu tabon laifinka yana nan a gabana,”in ji Ubangiji Mai Iko Duka.23“Yaya za ka ce, ‘Ban ƙazantu ba;ban bi Ba’al ba’?Duba yadda ka yi a cikin kwari;ka ga abin da ka yi.Kai kamar makwaɗaciyar raƙuma ce mai zafin gudukana gudu nan da can,24kamar jakar jejin da ta saba da hamada,mai busar iska cikin son barbarantasa’ad da take son barbara wa zai iya hana ta?Jakin da yake nemanta, ba ya bukatar wahalar da kansa;a lokacin barbara za a same ta.25Kada ka yi gudu har ƙafafunka su zama ba takalmamaƙogwaronka kuma ya bushe.Amma sai ka ce, ‘Ba amfani!Ina ƙaunar baƙin allolikuma dole in bi su.’26“Kamar yadda akan kunyatar da ɓarawo sa’ad da aka kama shi,haka gidan Isra’ila zai sha kunya,su, sarakunansu da shugabanninsu,firistocinsu da kuma annabawansu.27Kuna ce wa itace, ‘Kai ne mahaifina,’ga dutse kuma, ‘Kai ne ka haife ni.’Sun juye mini bayansuba fuskokinsu ba;duk da haka sa’ad da suna cikin wahala, sukan ce,‘Zo ka cece mu!’28To ina allolin da kuka yi wa kanku?Bari su zo in suna iya cetonkusa’ad da kuke cikin wahala!Gama kuna da alloli masu yawakamar yadda kuke da garuruwa, ya Yahuda.29“Me ya sa kuke tuhumana?Dukanku kun yi mini tawaye,”in ji Ubangiji.30“A banza na hukunta mutanenku;ba su yi gyara ba.Takobinku ya cinye annabawankukamar zaki mai jin yunwa.31“Ku na wannan zamani, ku saurari maganar Ubangiji.“Na zama wa Isra’ila hamada neko ƙasa mai babban duhu?Me ya sa mutanena suke cewa, ‘Muna da ’yanci mu yi ta yawo;ba za mu ƙara zuwa wurinka ba’?32Budurwa za tă manta da kayan adontaamarya ta manta da kayan adon aurenta?Duk da haka mutanena sun manta da ni,kwanaki ba iyaka.33Kuna da azanci sosai a bin masoya!Kai, ko mafiya muni cikin mata tana iya koya daga hanyoyinku.34A rigunanku mutane kan samijinin matalauta marasa laifi,ko da yake ba ku kama su suna fasawa su shiga ba.Duk da haka35kuna cewa, ‘Ba ni da laifi;ba ya fushi da ni.’Amma zan zartar da hukunci a kankudomin kun ce, ‘Ban yi zunubi ba.’36Don me kuke yawo da yawa haka,kuna ta canjin hanyoyinku?Masar za tă kunyata kuyadda kuka sha kunya a wurin Assuriya.37Za ku kuma bar wurinda hannuwanku a kanku,gama Ubangiji ya ƙi waɗanda kuka amince da su;ba za ku zama abin taimako a gare su ba.