Irmiya17hau_bib
1“An rubuta zunubin Yahuda da alƙalamin ƙarfe,an rubuta da tsinin dutse,a kan allunan zukatansuda kuma a kan ƙahonin bagadansu.2Har ’ya’yansu ma sun tunabagadansu da ginshiƙan Asheransukusa da itatuwa masu duhuwada kuma a kan tuddai masu tsayi.3Dutsena a ƙasarda dukiyarku na ƙasar da dukan arzikinkuza a ba da su ganima,tare da masujadanku na kan tuddai,saboda zunubi ko’ina a ƙasarku.4Saboda laifinku za ku rasagādon da na ba ku.Zan bautar da ku ga abokan gābankua ƙasar da ba ku sani ba,domin kun husata ni,zai kuwa ci har abada.”5Ga abin da Ubangiji yana cewa,“La’ananne ne mutumin da yake dogara ga mutum,wanda ya dogara ga jiki don ƙarfiwanda kuma zuciyarsa ta juya wa Ubangiji baya.6Zai zama kamar ɗan kurmi a ƙasar da take kango;ba za su ga arziki sa’ad da ya zo ba.Za su zauna a busassun wuraren hamada,a cikin ƙasar gishiri inda ba kowa.7“Amma mai albarka ne mutumin da yake dogara ga Ubangiji,wanda ƙarfin halinsa yana daga Ubangiji.8Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwawanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi.Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo;ganyayensa kullum kore suke.Ba shi da damuwa a shekarar făriba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”9Zuciya ta fi kome ruɗuta fi ƙarfin warkewa.Wa zai iya gane ta?10“Ni Ubangiji nakan bincike zuciyain gwada tunani,don in sāka wa kowane mutum bisa ga halinsa,bisa ga ayyukansa.”11Kamar makwarwar da ta kwanta a kan ƙwan da ba ita ta zuba bahaka yake da mutumin da ya sami arziki a hanyar da ba daidai ba.A tsakiyar rayuwarsa za su rabu da shi,a ƙarshe kuma zai zama wawa.12Kursiyi mai daraja, da aka ɗaukaka tun daga farko,shi ne wuri mai tsarkinmu.13Ya Ubangiji, sa zuciyar Isra’ila,duk waɗanda suka rabu da kai za su sha kunya.Waɗanda suka juya maka baya za a rubuta su a ƙuradomin sun yashe Ubangiji,maɓulɓular ruwan rai.14Ka warkar da ni, ya Ubangiji, zan kuwa warke;ka cece ni zan kuwa cetu,gama kai ne nake yabo.15Sun riƙa ce mini, “Ina maganar Ubangiji take?Bari tă cika yanzu!”16Ban gudu zaman mai yin maka kiwo ba;ka sani ban marmarin ranan nan ta masifa ba.Abin da ya fito daga leɓunana kuwa, a bayyane suke gare ka.17Kada ka zama mini abin razana;kai ne mafakata a ranar masifa.18Bari masu tsananta mini su sha kunya,amma ka kiyaye ni daga shan kunya;bari su tsorata,amma ka kiyaye ni da razana.Ka kawo musu ranar masifa;ka hallaka su da hallaka riɓi biyu.