Irmiya12hau_bib

Damuwar Irmiya

1Kullum kai mai adalci ne, ya Ubangiji,sa’ad da na kawo ƙara a gabanka.Duk da haka zan yi magana da kai game da shari’arka.Me ya sa mugaye suke nasara?Me ya sa dukan maciya amana suke zama ba damuwa?2Ka dasa su, sun kuwa yi saiwa;sun yi girma suna ba da ’ya’ya.Kullum sunanka yana a bakinsuamma kana nesa da zuciyarsu.3Duk da haka ka san ni, ya Ubangiji;kana ganina ka kuma gwada tunanina game da kai.Ka ja su kamar tumakin da za a yanka!Ka ware su don ranar yanka!4Har yaushe ƙasar za tă kasance busasshiyaciyawar kowane fili ta bushe?Domin waɗanda suke zaune cikinta mugaye ne,dabbobi da tsuntsaye sun hallaka.Ban da haka ma, mutane suna cewa,“Ba zai ga abin da yake faruwa da mu ba.”

Amsar Allah

5“In ka yi tsere da mutane a ƙafasuka kuma gajiyar da kai,yaya za ka yi gasa da dawakai?In ka yi tuntuɓe a lafiyayyiyar ƙasa,ƙaƙa za ka yi a kurmin Urdun?6’Yan’uwanka, iyalinka har su ma sun bashe ka;sun tā da kuka mai ƙarfi a kanka.Kada ka amince da su,ko da yake suna faɗa maganganu masu kyau game da kai.
7“Zan yashe gidana,in rabu da gādona;Zan ba da wadda nake ƙaunaa hannuwan abokan gābanta.8Gādona ya zama minikamar zaki a kurmi.Yana mini ruri;saboda haka na ƙi shi.9Ashe, gādona bai zama minikamar dabbare dabbaren tsuntsu mai cin namada sauran tsuntsaye masu cin nama suka kewaye shi da faɗa ba?Tafi ka tattaro dukan namun jeji;ka kawo su su ci.10Makiyaya masu yawa za su lalace gonar inabinasu tattake gonata;za su mai da gonata mai kyaukango marar amfani.11Za tă zama kango,busasshiya da kuma kango a gabana;ƙasar duka za tă zama kangodomin ba wanda ya kula.12A kan dukan tsaunukan nan na hamadamasu hallakarwa za su zo,gama takobin Ubangiji zai cidaga wannan iyaka ƙasa zuwa wancan;ba wanda zai zauna lafiya.13Za su shuka alkama, su girbe ƙayayyuwa;za su gajiyar da kansu, ba za su kuwa sami kome ba.Saboda haka ku sha kunyar abin da kuka girbesaboda zafin fushin Ubangiji.”14Ga abin da Ubangiji yana cewa, “Game da dukan mugayen maƙwabtana waɗanda suka ƙwace gādon da na ba wa mutanena Isra’ila kuwa, zan tumɓuke su daga ƙasashensu zan kuma tumɓuke gidan Yahuda daga cikinsu.15Amma bayan na tumɓuke su, zan sāke jin tausayi in komo da kowannensu zuwa gādonsa da kuma ƙasarsa.16In kuma suka koyi al’amuran mutanena sosai suka kuma yi rantsuwa da sunana, suna cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye’ kamar yadda sun taɓa koya wa jama’ata yin rantsuwa da Ba’al, sa’an nan za su kahu a cikin jama’ata.17Amma duk al’ummar da ba tă saurara ba, zan tumɓuke ta ɗungum in kuma hallaka ta,” in ji Ubangiji.