Irmiya1hau_bib
1Kalmomin Irmiya ɗan Hilkiya, ɗaya daga cikin firistoci a Anatot a yankin Benyamin.2Maganar Ubangiji ta zo gare shi a shekara ta goma sha uku ta sarautar Yosiya ɗan Amon sarkin Yahuda,3da kuma a zamanin Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda, har zuwa watan biyar na shekara goma sha ɗaya na Zedekiya ɗan Yosiya sarkin Yahuda, sa’ad da aka kai mutanen Urushalima zaman bauta.