1Ruhun Ubangiji Mai Iko Duka yana a kaina,domin Ubangiji ya shafe nidomin in yi wa’azi labari mai daɗi ga matalauta.Ya aiko ni in warkar da waɗanda suka karai a zuci,don in yi shelar ’yanci don ɗaurarruin kuma kunce ’yan kurkuku daga duhu2don in yi shelar shekarar tagomashin Ubangijida kuma ranar ɗaukan fansar Allahnmu,don in ta’azantar da dukan waɗanda suke makoki,3in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona,in maido musu rawani mai kyaua maimako na toka,man murnaa maimako na makoki,da kuma rigar yaboa maimako na ruhun fid da zuciya.Za a ce da su itatuwan oak na adalci,shukin Ubangijidon bayyana darajarsa.4Za su sāke gina kufai na dāsu raya wurare da aka lalace tun da daɗewa;za su sabunta biranen da aka rurrusheda aka lalace tun zamanai masu yawa da suka wuce.5Baƙi za su yi kiwon garkunanki;baƙi za su yi miki noman gonaki da gonakin inabinki.6Za a kuma kira ku firistocin Ubangiji,za a kira ku masu hidimar Allahnmu.Za ku ci wadatar waɗansu al’ummai,kuma a cikin dukiyarsu za ku yi taƙama.7A maimakon kunyarsumutanena za su sami rabi riɓi biyu,a maimakon wulaƙanciza su yi farin ciki cikin gādonsu;ta haka za su gāji rabo riɓi biyu a ƙasarsu,da kuma madawwamin farin ciki zai zama nasu.8“Gama ni, Ubangiji, ina ƙaunar adalci;na ƙi fashi da aikata laifi.Cikin adalcina zan sāka musuin kuma yi madawwamin alkawari da su.9Za a san da zuriyarsu a cikin al’ummai’ya’yansu kuma a cikin mutane.Dukan waɗanda suka gan su za su sancewa su mutane ne da Ubangiji ya sa wa albarka.”10Ina jin daɗi ƙwarai a cikin Ubangiji;raina yana farin ciki a cikin Allahna.Gama ya suturce ni da rigunan cetoya yi mini ado da rigar adalci,yadda ango yakan yi wa kansa ado kamar firistkamar kuma yadda amarya takan sha ado da duwatsunta masu daraja.11Gama kamar yadda ƙasa takan sa tsire-tsire su tohulambu kuma ya sa iri ya yi girma,haka Ubangiji Mai Iko Duka zai sa adalci da yabosu tsiro a gaban dukan al’ummai.