Ishaya57hau_bib
1Mai adalci yakan mutu,ba kuwa wanda yakan yi tunani a zuciyarsa;an kwashe mutanen kirki,ba kuwa wanda ya fahimtacewa an kwashe masu adalcidon a tsame su daga mugunta.2Waɗanda suke aikata abin da yake daidaisukan shiga da salama;sukan huta yayinda suka kwanta cikin kabari.3“Amma ku, ku matso nan, ku ’ya’ya maza na masu sihiri,ku zuriyar mazinata da karuwai!4Wane ne kuke yi wa ba’a?Ga wa kuke masa gwalokuna kuma fitar da harshe?Ashe, ku ba tarin ’yan tawaye ba ne,zuriyar maƙaryata?5Kuna cike da muguwar sha’awa mai ƙonawa a cikin itatuwan oakda kuma a ƙarƙashin kowane itace mai inuwa;kuna miƙa hadayar ’ya’yanku a rafuffukada kuma a ƙarƙashin tsagaggun duwatsu.6Gumakan da suke cikin duwatsu masu sulɓi su ne rabonku;su ɗin, su ne rabonku.I, gare su kuka kwarara hadayu na shakuka kuma miƙa hadayu na gari.Saboda waɗannan abubuwa, zan yi haƙuri?7Kun yi gadonku a dogayen duwatsu masu tsayi da kuma a tudu mai tsawo;a can kuka haura don ku miƙa hadayunku.8A bayan ƙofofi da madogaran ƙofofikuka kafa alamun gumakanku.Kuka yashe ni, kuka kware gadonku,kuka kwanta a kansa kuka fadada shi;kuka kuma ƙulla yarjejjeniya da waɗanda kuke ƙaunar gadajensu,kuka dubi tsiraicinsu.9Kuka tafi wurin Molek da man zaitunkuka kuma riɓaɓɓanya turarenku.Kuka aika jakadunku can da nisa;kuka gangara zuwa cikin kabari kansa!10Kuka gaji cikin dukan al’amuranku,amma ba ku iya cewa, ‘Aikin banza ne ba.’Kuka sami sabuntar ƙarfinku,ta haka ba ku suma ba.11“Wa ya sa ku fargaba, kuna jin tsorohar kuka yi mini ƙarya,ba ku kuma tuna da ni baballe ku yi tunanin wannan a zukatanku?Ba don na daɗe ina shiru ba neya sa ba kwa tsorona?12Zan bayyana adalcinku da kuma ayyukanku,ba kuwa za su amfane ku ba.13Sa’ad da kuka nemi taimako,bari tarin gumakanku su cece ku!Iska za tă kwashe dukansu tă tafi,ɗan numfashi kawai zai hura su.Amma mutumin da ya mai da ni mafakarsazai gāji ƙasarya kuma mallaki dutsena mai tsarki.”