Ishaya56hau_bib

Ceto domin waɗansu

1Ga abin da Ubangiji yana cewa,“Ku riƙe gaskiyaku yi abin da yake daidai,gama cetona yana kusaza a kuma bayyana adalcina nan da nan.2Mai albarka ne mutumin da ya aikata wannan,mutumin da ya riƙe kamyana kiyaye Asabbaci ba tare da ƙazantar da shi ba,yana kuma kiyaye kansa daga yin mugun abu.”
3Kada baƙon da ya miƙa kansa ga Ubangiji ya ce,“Ai Ubangiji zai ware ni daga mutanensa.”Kada kuma wani bābā ya yi gunaguni cewa,“Ni busasshen itace ne kawai.”4Gama ga abin da Ubangiji ya faɗa,“Wa bābānnin da suna kiyaye Asabbatai,waɗanda suka zaɓi yin abin da ya gamshe nisuna kuma riƙe da alkawarina kankan,5a gare su cikin haikalina da kuma bangayensazan ba da matuni da kuma sunamafi kyau fiye da ’ya’ya maza da kuma ’ya’ya mata;zan ba su madawwamin sunanda ba za a raba su da shi ba.6Baƙin da suka miƙa kansu ga Ubangijidon su bauta masa,su kuma ƙaunaci sunan Ubangiji,waɗanda kuma suke yin masa sujada,duk waɗanda suka kiyaye Asabbaci ba tare da ƙazantar da shi basuka kuma riƙe alkawarina kankan,7waɗannan ne zan kai tsattsarkan dutsenain sa su yi farin ciki a gidana na addu’a.Hadayunsu na ƙonawa da sadakokinsuza su zama abin karɓa a bagadena;gama za a ce da gidanagidan addu’a domin dukan al’ummai.”8Ubangiji Mai Iko Duka ya furta cewa,zai tattara korarru na Isra’ila,“Zan ƙara tattaro waɗansubayan waɗanda na riga na tattara.”

Zargin da Allah ya yi a kan mugaye

9Ku zo, dukanku namun jeji,ku zo ku ci, dukanku namun jeji!10Matsaran Isra’ila makafi ne,dukansu jahilai ne;dukansu bebayen karnuka neba za su iya haushi ba;suna kwance ne kawai suna mafarki,suna son barci ba dama.11Su karnuka ne masu kwaɗayi;ba su taɓa ƙoshi.Su makiyaya ne marasa ganewa;duk sun nufi inda suka ga dama,kowa yana nemar wa kansa riba.12Kowanne yakan ce, “Zo, bari in samo ruwan inabi!Bari mu cika cikinmu da barasa!Gobe ma zai zama kamar yau,ko ma fiye da haka.”