Ishaya52hau_bib
1Ki farka, ki farka, ya Sihiyona,ki sanya wa kanki ƙarfi.Ki sa rigarki na daraja,Ya Urushalima, birni mai tsarki.Marasa kaciya da maƙazantaba za su shi cikinki ba.2Ki kakkaɓe ƙurarki;ki tashi, ki zauna a kursiyinki, ya Urushalima.Ki ’yantar da kanki daga sarƙoƙi a wuyanki,Ke kamammiyar Diyar Sihiyona.3Gama ga abin Ubangiji yana cewa,“An sayar da ke ba da kuɗi ba,kuma ba da kuɗi za a fanshe ki ba.”4Gama ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,“Da farko mutanena suka gangara zuwa Masar don su zauna;a baya-bayan nan, Assuriya sun zalunce su.5“Yanzu kuma me nake da shi a nan?”In ji Ubangiji.“Gama an kwashe mutanena ba a bakin kome bakuma waɗanda suka mallake su sun yi musu ba’a,Kullum ana cin gaba da yin wa sunana saɓo.6Saboda haka mutanena za su san sunana;saboda haka a wannan rana za su sancewa ni ne wanda ya faɗa wannan.I, ni ne.”7Me ya fi wannan kyau a kan duwatsua ga ƙafafu na masu kawo labari mai daɗiwaɗanda suke shelar salama,waɗanda suke kawo labari mai daɗi,waɗanda suke shelar ceto,waɗanda suke ce wa Sihiyona,“Allahnki yana mulki!”8Ki kasa kunne! Masu tsaronki sun tā da muryoyinsu;tare sun yi sowa ta farin ciki.Sa’ad da Ubangiji ya komo Sihiyona,za su gan shi da idanunsu.9Ku ɓarke cikin waƙoƙin farin ciki gaba ɗaya,kangonki na Urushalima,gama Ubangiji ya ta’azantar da mutanensa,ya fanshi Urushalima.10Ubangiji zai nuna hannunsa mai tsarki a filia idanun dukan al’ummai,da kuma dukan iyakokin duniya za su ganiceton Allahnmu.11Ku fita, ku fita daga can!Kada ku taɓa wani abu marar tsarki!Ku fita daga cikinta ku zama da tsarki,ku da kuke ɗaukan kayan aikin Ubangiji.12Amma ba za ku fita a gaggauce bako ku tafi da gudu;gama Ubangiji zai ja gabanku,Allah na Isra’ila zai kasance mai tsaron bayanku.