1Zan rera waƙa wa ƙaunataccenawaƙa game da gonar inabinsa.Ƙaunataccena yana da gonar inabia gefen tudu mai dausayi.2Ya haƙa ƙasa ya kuma tsintsince duwatsunya shuka mata inabi mafi kyau.Ya gina hasumiyar tsaro a cikintaya kuma shirya wurin matsin ruwan inabi.Sa’an nan ya sa rai ga samun girbi mai kyau na inabin,amma sai ga shi inabin ya ba da munanan ’ya’ya.3“Yanzu fa ku mazauna cikin Urushalima da mutanen Yahuda,ku shari’anta tsakanina da gonar inabina.4Me kuma ya rage da za a yi wa gonar inabinafiye da abin da na yi mata?Da na nemi inabi masu kyau,me ya sa ta ba da munana ’ya’ya?5Yanzu zan faɗa mukuabin da zan yi da gonar inabina.Zan cire katangar da ta kewaye ta,za tă kuwa lalace;zan rushe bangonta,za a kuwa tattake ta.6Zan mai da ita kango,ba zan aske ta ba, ba kuwa zan nome ta ba,sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa kuwa za su yi girma a canZan umarci gizagizaikada su yi ruwan sama a kanta.”7Gonar inabin Ubangiji Maɗaukakiita ce gidan Isra’ila,mutanen Yahuda kumasu ne lambun farin cikinsa.Yana kuma nema ganin gaskiya, amma sai ga zub da jini;yana neman adalci, amma sai ga shi kukan azaba yake ji.
Kaito da hukunce-hukunce
8Kaitonku ku waɗanda kuke ƙara wa kanku gidajekuke kuma haɗa gonaki da gonakihar babu sauran filin da ya rageku kuma zauna ku kaɗai a ƙasar.9Ubangiji Maɗaukaki ya furta a kunnuwana,“Tabbatacce manyan gidajen za su zama kango,za a bar kyawawan gidajen nan ba kowa.10Kadada goma na gonar inabi zai ba da garwan ruwan inabi ɗaya kaɗai,mudu guda na iri kuma zai ba da efa na hatsi guda kurum.”11Kaiton waɗanda suke tashi da sassafedon su nufi wurin shaye-shaye,waɗanda suke raba darehar sai sun bugu da ruwan inabi.12Suna kaɗa garaya, da molaye a bukukkuwansu,ganguna da busa da ruwan inabi,amma ba su kula da ayyukan Ubangiji ba,ba sa biyayya ga aikin hannuwansa.13Saboda haka mutanena za su yi zaman bautadomin rashin fahimi;manyan mutanensu za su mutu da yunwatalakawansu kuma su mutu da ƙishirwa.14Saboda haka kabari ya fadada marmarinsaya kuma buɗe bakinsa babu iyaka;cikinsa manyan mutanensu da talakawansu za su gangaratare da dukan masu hayaniyarsu da masu murnansu.15Ta haka za a ƙasƙantar da mutumkuma za a ƙasƙantar da ’yan adam,za a ƙasƙanta da masu girman kai.16Amma Ubangiji Maɗaukaki zai sami ɗaukaka ta wurin aikata gaskiya,kuma Allah mai tsarki zai nuna kansa ta wurin adalcinsa.17Sa’an nan tumaki za su yi kiwo kamar yadda suke yi a wurin kiwonsu;raguna za su yi kiwo cikin abubuwa masu kyau da suka lalace.18Kaiton waɗanda suke jan zunubi da igiyar ruɗu,da kuma mugunta da igiyoyin keken yaƙin,19waɗanda suke cewa, “Bari Allah yă gaggauta,bari yă hanzarta aikinsadon mu gani.Bari yă iso,bari shirin Mai Tsarkin nan na Isra’ila yă zo,don mu sani.”20Kaiton waɗanda suke ce da mugunta nagartanagarta kuma mugunta,waɗanda suke mai da duhu haskehaske kuma duhu,waɗanda suke mai da ɗaci zaƙizaƙi kuma ɗaci.21Kaiton waɗanda suke tsammani suna da hikimada kuma wayo a idonsu.22Kaiton waɗanda suke jarumawa a shan ruwan inabida gwanaye a haɗin abubuwan sha,23waɗanda suke ƙyale masu laifi don sun ba da cin hanci,amma su hana a yi gaskiya wa marasa laifi.24Saboda haka kamar yadda harshen wuta yakan lashe karakuma kamar yadda busasshiyar ciyawa takan ƙone ƙurmus a cikin wuta,haka saiwarsu za su ruɓaiska kuma ta hura furanninsu kamar ƙura;gama sun ƙi dokar Ubangiji Maɗaukakisuka kuma ƙyale maganar Mai Tsarkin nan na Isra’ila.25Saboda haka fushin Ubangiji ya yi ƙuna a kan mutanensa;ya ɗaga hannunsa ya kuma buge su.Duwatsu sun jijjigu,gawawwaki kuwa suka zama kamar juji a tituna.Saboda wannan duka, fushinsa bai huce ba,bai kuwa janye hannunsa ba.26Ya ɗaga tuta don al’ummai masu nisa,ya yi feɗuwa wa waɗanda suke a iyakar duniya.Ga shi sun iso,da sauri da kuma gaggawa!27Babu ko ɗayansu da ya gaji ko ya yi tuntuɓe,babu ko ɗaya da ya yi gyangyaɗi ko barci;babu abin ɗamarar da ya kunce a gindi,ba igiyar takalmin da ta tsinke.28Kibiyoyinsu masu tsini ne,an ɗaura dukan bakkunansu;kofatan dawakansu sun yi kamar dutsen ƙanƙara,ƙafafun keken yaƙinsu kamar guguwa ne.29Rurinsu ya yi kamar na zaki,suna ruri kamar ’yan zakoki;suna yin gurnani yayinda suke kamun abin da suke farautasu ɗauke shi ba mai ƙwace shi.30A wannan rana za su yi ta ruri a kansakamar rurin teku.Kuma in wani ya dubi ƙasar,zai ga duhu da damuwa;haske ma zai zama duhu ta wurin gizagizai.