1“Ki gangara, ki zauna a ƙura,Budurwa Diyar Babilon;ki zauna a ƙasa ba tare da rawani ba,Diyar Babiloniyawa.Ba za a ƙara kira ke marar ƙarfi ’yar gata ba.2Ɗauki dutsen niƙa ki niƙa gari;ki kware lulluɓinki.Ki ɗaga fatarinki ki bar ƙafafunki tsirara,ki kuma yi ta ratsa cikin rafuffuka.3Tsirararki zai bayyanaza a kuma buɗe kunyarki.Zan ɗauki fansa;ba zan bar wani ba.”4Mai Fansarmu, Ubangiji Maɗaukaki shi ne sunansa,shi ne Mai Tsarkin nan na Isra’ila.5“Zauna shiru, tafi cikin duhu,Diyar Babiloniya;ba za a ƙara kira kesarauniyar masarautai.6Na yi fushi da mutanenana ƙazantar da gādona;na ba su ga hannunki,ba ki kuwa nuna musu jinƙai ba.Har ma da tsofaffikin jibga musu kaya masu nauyi sosai.7Kika ce, ‘Zan ci gaba har abada,madawwamiyar sarauniya!’Amma ba ki lura da waɗannan abubuwako ki yi la’akari a kan abin da zai faru ba.8“To, yanzu fa, ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi,mai zama da rai kwancekina kuma ce wa kanki,‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni.Ba zan taɓa zama gwauruwako in sha wahalar rashin ’ya’ya ba.’9Duk waɗannan za su sha kankicikin farat ɗaya, a rana guda,rashin ’ya’ya da gwauranci.Za su zo a kanki da cikakken minzani,duk da yawan masu dubankida kuma dukan sihirinki.10Kin dogara a muguntarkikika kuma ce, ‘Babu wanda ya gan ni.’Hikimarki da saninki sun ɓad da kesa’ad da kika ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni.’11Bala’i zai fāɗo a kanki,kuma ba za ki san yadda za ki rinjaye shi yă janye ba.Masifa za tă fāɗo a kankida ba za ki iya tsai da ita da kuɗin fansa ba;lalacewar da ba ki taɓa mafarkinta baza tă auko miki nan da nan.12“Ki dai ci gaba, da sihirinkida kuma makarunki masu yawa,waɗanda kika yi ta wahala tun kina jaririya.Mai yiwuwa ki yi nasara,mai yiwuwa ki jawo fargaba.13Dukan shawarwarin da kika samu sun dai gajiyar da ke ne kawai!Bari masananki na taurari su zo gaba,waɗannan masu zāna taswirar sammai suna kuma faɗa miki dukan abin da zai faru da ke wata-wata,bari su cece ki daga abin da zai faru da ke.14Tabbas suna kama da bunnu;wuta za tă cinye su ƙaf.Ba za su ma iya ceton kansudaga ikon wutar ba.Ba wutar da wani zai ji ɗumi;ba wutar da za a zauna kusa da ita.15Abin da za su iya yi miki ke nan kawai,waɗannan da kika yi ta fama da sukika kuma yi ciniki da su tun kina jaririya.Kowannensu zai tafi cikin kuskurensa;babu ko ɗayan da zai cece ki.