Ishaya42hau_bib

Bawan Ubangiji

1“Ga bawana, wanda na ɗaukaka,zaɓaɓɓen nan nawa wanda nake jin daɗi;Zan sa Ruhuna a cikinsazai kuwa kawo adalci ga al’ummai.2Ba zai yi ihu ko ya tā da murya,ko ya daga muryarsa a tituna ba.3Iwan da ta tanƙware ba zai karye ba,ba zai kashe lagwani mai hayaƙi ba.Cikin aminci zai kawo adalci;4ba zai kāsa ko ya karai basai ya kafa adalci a duniya.Cikin dokarsa tsibirai za su sa zuciya.”
5Ga abin da Allah Ubangiji ya ce,shi da ya halicci sammai ya kuma miƙe su,wanda ya shimfiɗa duniya da dukan abin da ya fito cikinta,wanda ya ba wa mutanenta numfashi,da rai ga waɗanda suke tafiya a kanta.6“Ni Ubangiji, na kira ka cikin adalci;zan riƙe hannunka.Zan kiyaye ka in kuma sa kazama alkawari ga mutanehaske kuma ga Al’ummai,7don ka buɗe idanun makafika ’yantar da kamammu daga kurkukukuma kunce ɗaurarrun kurkuku masu zama cikin duhu.
8“Ni ne Ubangiji; sunana ke nan!Ba zan ba da ɗaukakata ga wani ba ko yabona ga gumaka.9Duba, abubuwan da sun tabbata,sababbin abubuwa kuwa nake furtawa;kafin ma su soma faruwana sanar da su gare ku.”

Waƙar yabo ga Ubangiji

10Ku rera sabuwar waƙa ga Ubangiji,ku yi yabonsa daga iyakar duniya,ku da kuka gangara zuwa teku, da kome da yake cikinsa,ku tsibirai, da waɗanda suke zama a cikinsu.11Bari hamada da garuruwanta su tā da muryoyinsu;bari wuraren zaman da Kedar ke zama su yi farin ciki.Bari mutanen Sela su rera don farin ciki;bari su yi sowa daga ƙwanƙolin duwatsu.12Bari su ɗaukaka Ubangijisu kuma yi shelar yabonsa a tsibirai.13Ubangiji zai fita ya yi yaƙi kamar mai ƙarfi,kamar jarumi zai yi himma;da ihu zai tā da kirarin yaƙizai kuma yi nasara a kan abokan gābansa.
14“Na daɗe ina shiru,na yi shiru na kuma ƙame kaina.Amma yanzu, kamar mace mai naƙuda,na yi ƙara, ina nishi ina kuma haki.15Zan lalatar da duwatsu da tuddaiin busar da dukan itatuwansu;zan mai da koguna su zama tsibiraiin kuma busar da tafkuna.16Zan yi wa makafi jagora a hanyoyin da ba su taɓa sani ba,a hanyoyin da ba a saba ba zan bishe su;zan mai da duhu ya zama haske a gabansuin kuma mai da ƙasa mai kururrumai ta zama sumul.Abubuwan da zan yi ke nan;ba zan yashe su ba.17Amma waɗanda suka dogara ga gumaka,waɗanda suke ce wa siffofi, ‘Ku ne allolinmu,’za a mai da su baya da kunya.

Isra’ila makaho da kuma kurma

18“Ka ji, kai kurma;duba, kai makaho, ka kuma gani!19Wane ne makaho in ba bawana ba,da kuma kurma in ba ɗan aikan da na aika ba?Wane ne makaho kamar wanda ya miƙa kai gare ni,makaho kamar bawan Ubangiji?20Kun ga abubuwa masu yawa, amma ba ku kula ba;kunnuwanku suna a buɗe, amma ba kwa jin wani abu.”21Yakan gamsar da Ubangijisaboda adalcinsaya sa dokarsa ta zama mai girma da kuma mai ɗaukaka.22Amma ga mutanen da aka washe aka kuma kwashe ganima,an yi wa dukansu tarko a cikin rammukako kuma an ɓoye su cikin kurkuku.Sun zama ganima,babu wani da zai kuɓutar da su;an mai da su ganima,ba wanda zai ce, “Mayar da su.”
23Wane ne a cikinku zai saurari wannanko ya kasa kunne sosai a cikin kwanaki masu zuwa?24Wa ya ba da Yaƙub don yă zama ganimaIsra’ila kuma ga masu kwasar ganima?Ba Ubangiji ba ne,wanda kuka yi wa zunubi?Gama ba su bi hanyoyinsa ba;ba su yi biyayya da dokarsa ba.25Saboda haka ya zuba musu zafin fushinsa,yaƙi mai tsanani.Ya rufe su cikin harsunan wuta, duk da haka ba su gane ba;ya cinye su, amma ba su koyi kome ba.