1Kaiton waɗanda suka gangara zuwa Masar don neman taimako,waɗanda suke dogara ga dawakai,waɗanda suke dogara ga yawan kekunan yaƙinsuda kuma a girman ƙarfin mahayan dawakansu,amma ba sa dogara ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila,ko ya nemi taimako daga Ubangiji.2Shi ma yana da hikima kuma zai iya kawo masifa;ba ya janye kalmominsa.Zai yi gāba da gidan mugu,gāba da waɗanda suke taimakon masu aikata mugunta.3Amma Masarawa mutane ne ba Allah ba;dawakansu nama da jini ne ba ruhu ba.Sa’ad da Ubangiji ya miƙa hannunsa,shi da yake taimako zai yi tuntuɓeshi da aka taimaka zai fāɗi;dukansu biyu za su hallaka tare.4Ga abin da Ubangiji ya faɗa mini,“Kamar yadda zaki kan yi ruribabban zaki a kan abin da ya yi farauta,kuma ko da yake dukan ƙungiyar makiyayasun taru wuri ɗaya a kansa,ba zai jijjigu ta wurin ihunsu bako ya damu da kiraye-kirayensu,ta haka Ubangiji Maɗaukaki zai saukodon yă yi yaƙi a kan Dutsen Sihiyona da kuma a kan ƙwanƙolinsa.5Kamar tsuntsaye masu shawagi a samahaka Ubangiji Maɗaukaki zai kiyaye Urushalima;zai kāre ta ya kuma fanshe ta,zai ‘ƙetare’ ta ya kuma kuɓutar da ita.”6Ku dawo gare shi ku da kuka yi masa babban tayarwa, ya Isra’ilawa.7Gama a wannan rana kowannenku zai ƙi gumakan azurfa da zinariya da hannuwanku masu zunubi suka yi.8“Za a karkashe Assuriyawa da takobin da ba na yin mutum ba;takobi, da ba na yin mutum ba, zai cinye.Za su gudu daga takobiza a kuma sa samarinsu aikin dole.9Kagararsu za tă fāɗi saboda razana;da ganin matsayin yaƙin, shugabannin yaƙinsu za su firgita,”in ji Ubangiji,wanda wutarsa tana a Sihiyona,wanda matoyarsa tana a Urushalima.