1Kaito ga wannan rawani, girman kai na mashayan Efraim,ga fure mai yanƙwanewa, darajar kyansa,da aka sa a kan kwari mai ba da amfani,ga birnin nan, wadda take girman kan waɗanda aka ƙasƙantar da ruwan inabinsu!2Duba, Ubangiji yana da wanda yake da iko da kuma ƙarfi.Kamar dutsen ƙanƙara da kuma iska mai ɓarna,kamar kwararowar ruwa da rigyawa mai kirmewa,zai jefa shi har ƙasa da ƙarfi.3Za a tattaka wannan rawani,girman kai na mashayan Efraim da ƙafa.4Wannan fure mai yanƙwanewa, darajarar kyansa,da aka sa a kan kwari mai ba da amfani,zai zama kamar ’ya’yan ɓaure, nunan fari,da zarar wani ya gani ya kuma tsinka,zai haɗiye shi.5A wannan rana Ubangiji Maɗaukakizai zama rawani mai darajakyakkyawan rawaniwa mutanensa da suka ragu.6Zai zama ruhun adalcigare shi wanda yake zaune a kujerar shari’a,wurin samun ƙarfiga waɗanda suka kori abokan gāban da suka fāɗa musu da yaƙi a ƙofofi.7Da waɗannan kuma masu tangaɗi saboda sun sha ruwan inabisuke jiri don sun sha barasaFiristoci da annabawa suna tangaɗi saboda sun sha barasasun kuma yi tatur da ruwan inabi;suna jiri saboda sun sha barasa,suna tangaɗi sa’ad da suke ganin wahayi,suna tuntuɓe sa’ad da suke ba da shawara.8Duk amai ya rufe teburorikuma babu wani wurin da ba a ɓata ba.9“Wane ne yake so ya koyar?Ga wa yake bayyana saƙonsa?Ga yaran da aka yaye,ga waɗanda ba a daɗe da yayewa ba ne?10Gama haka yake.Yi ka kuma yi, yi ka kuma yi,mulki a kan mulki, mulki a kan mulki;nan kaɗan, can kaɗan.”11To da kyau, da leɓunan baƙi da ku harsunan da ba sani baAllah zai yi magana da wannan mutane,12waɗanda zai ce,“Wannan shi ne wurin hutu, bari waɗanda suka gaji su huta”;da kuma, “Wannan shi ne wurin wartsakewa”amma sun ƙi su saurara.13Saboda haka fa, maganar Ubangiji gare su za tă zama,Yi ka kuma yi, yi ka kuma yi,mulki akan mulki, mulki a kan mulki;nan kaɗan, can kaɗan,domin su tafi su kuma fāɗi da baya,su ji rauni a kuma kama su da tarko, a kai su zaman bauta.14Saboda haka ku saurari maganar Ubangiji, ku masu ba’aku da kuke mulkin wannan mutane a Urushalima.15Kuna fariya cewa, “Mun yi alkawari da mutuwa,mun kuma yi yarjejjeniya da kabari.Sa’ad da zafi ya ratsa,ba zai taɓa mu ba,gama mun mai da ƙarya mafakarmuruɗu kuma wurin ɓuyanmu.”16Saboda haka ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka ya ce,“Duba, na kafa dutse a Sihiyona,dutsen da aka gwada,dutsen kusurwa mai daraja don tabbataccen tushe;wanda ya dogara gare shi ba zai taɓa shan kunya ba.17Zan mai da gaskiya igiyar gwajiadalci kuma ɗan katakon gwajin ginin;ƙanƙara za tă share mafakarku,ƙarya, da ruwa kuma za su mamaye maɓuyanku.18Za a soke alkawarinku da mutuwa;yarjejjeniyarku da kabari ba zai zaunu ba.Sa’ad da zafi mai ɓarna ya ratsa,zai hallaka ku.19A duk sa’ad da ya zo;ko da safiya, ko dare ko kuma da rana,zai yi ta ratsawa yana kwasanku.”Za ku zama kamar mutuminda ya zama abin karin magana,20wanda ya yi ƙoƙari yă kwanta a gajeren gado,yă kuma rufa da ɗan siririn bargo.21Ubangiji zai tashi kamar yadda ya yi a Dutsen Feratsim,zai tā da kansa kamar a Kwarin Gibeyondon yă aikata aikinsa, aikinsa da ba a saba gani ba,yă kuma yi aikinsa, baƙon aikinsa.22Yanzu ku daina ba’arku,in ba haka ba sarƙoƙinku za su ƙara nauyi;Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, ya faɗa minigame da hallakar da aka ƙaddara a kan dukan ƙasar.23Ku saurara ku kuma ji muryata;ku kasa kunne ku kuma ji abin da na faɗa.24Sa’ad da manomi ya yi noma don shuki, yakan ci gaba da noma ne?Yakan ci gaba da sara yana yin kunyoyi a ƙasa ne?25Sa’ad da ya shirya wuri da kyau,ba yakan shuka kanumfari ya kuma yayyafa ɗaɗɗoya ba?Ba yakan shuka alkama a kunyoyinsasha’ir a kunyoyinsa,tamba kuma a filinsa ba?26Allahnsa ya umarce shiya kuma koya masa hanyar da take daidai.27Ba a bugan kanumfari da ƙaton sandako a yi ta jujjuye ƙafar keke a kan ɗaɗɗoya;akan buga kanumfari da siririn sandaɗaɗɗoya kuma da tsumagiya.28Dole a niƙa hatsi don a yi burodi;saboda haka mutum ba zai yi ta bugun alkama, har yă ɓata tsabar ba.Ya san yadda zai sussuke alkamarsa,ba tare da ya ɓata tsabarta ba.29Dukan wannan hikimar takan zo daga Ubangiji Maɗaukaki ne,shi da yake mashawarci mai banmamaki, mafifici kuma cikin hikima.