Ishaya2hau_bib

Dutsen Ubangiji

1Ga abin da Ishaya ɗan Amoz ya gani game da Yahuda da Urushalima.
2A kwanaki masu zuwaza a kafa dutsen haikalin Ubangijia matsayin babba cikin duwatsu;za a daga shi bisa tuddai,kuma dukan al’ummai za su bumbunto zuwa gare shi.3Mutane da yawa za su zo su ce,“Ku zo, bari mu haura zuwa dutsen Ubangiji,zuwa gidan Allah na Yaƙub.Zai koya mana hanyoyinsa,domin mu yi tafiya cikin hanyoyinsa.”Dokar za tă fito daga Sihiyona,maganar Ubangiji daga Urushalima.4Zai shari’anta tsakanin al’ummaizai kuma sulhunta faɗar mutane masu yawa.Za su mai da takubansu su zama garemanimāsunsu su zama wuƙaƙen askin itatuwa.Al’umma ba za tă ƙara ɗauki takobi a kan al’umma ba,ba kuwa za su ƙara yin horarwar yaƙi.
5Ki zo, ya gidan Yaƙub,bari mu yi tafiya a hasken Ubangiji.

Ranar Ubangiji

6Ka rabu da mutanenka,gidan Yaƙub.Sun cika da ayyukan sihiri da aka kawo daga Gabas;suna yin duba kamar Filistiyawasuna tafa hannuwa tare da marasa sanin Allah.7Ƙasarsu ta cika da azurfa da zinariya;dukiyarsu kuma ba iyaka.Ƙasarsu ta cika da dawakai;kekunan yaƙinsu kuma ba iyaka.8Ƙasarsu ta cika da gumaka;sukan rusuna ga aikin hannuwansu,ga abin da yatsotsinsu suka yi.9Saboda an jawo mutum ƙasaaka kuma ƙasƙantar da ɗan adam,kada ku gafarta musu.
10Ku tafi cikin duwatsu,ku ɓuya cikin ƙasadaga razanar Ubangijida kuma darajar ɗaukakarsa!11Za a ƙasƙantar da mai girman kaiza a kuma lalatar da fariyar masu ɗaga kai;Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana.
12Ubangiji Maɗaukaki yana da rana ajiyedomin dukan masu girman kai da masu fariyadomin dukan waɗanda aka ɗaukaka(zai kuwa ƙasƙantar da su),13domin dukan al’ul na Lebanon, masu tsayi da masu fariya,da kuma dukan itatuwan oak na Bashan,14domin dukan dogayen duwatsuda kuma tuddai masu tsayi,15domin kowace doguwar hasumiyada kowace katanga mai ƙarfi,16domin kowane jirgin ruwan kasuwancida kuma jirgi mafi girma mafi kyau.17Za a jawo mai girman kai ƙasaa kuma ƙasƙantar da mai ɗaga kai;Ubangiji kaɗai za a ɗaukaka a wannan rana,18za a kuma kawar da gumaka ƙaƙaf.
19Mutane za su gudu zuwa kogwannin duwatsuda kuma ramummuka a ƙasadaga razanar Ubangijida kuma darajar ɗaukakarsa,sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya.20A wannan rana mutane za su zubar wajaba da jamagegumakansu na azurfa da gumakansu na zinariyada suka yi don su bauta musu.21Za su gudu zuwa kogwannin duwatsuda kuma zuwa tsagaggun duwatsudaga razanar Ubangijida kuma darajar ɗaukakarsa,sa’ad da ya tashi don yă girgiza duniya.
22Ku daina dogara ga mutum,wanda numfashi ne kawai yake da shi a hancinsa.Wace daraja gare shi?