Ishaya14hau_bib
1Ubangiji zai yi wa Yaƙub jinƙai;zai sāke zaɓi Isra’ilayă kuma zaunar da su a ƙasarsu.Baƙi ma za su zo su zauna tare da susu haɗa kai da gidan Yaƙub.2Al’ummai za su ɗauke susu kuma kawo wurin da yake nasu.Gidan Isra’ila kuwa za tă mallaki al’ummaia matsayin bayi maza da mata a ƙasar Ubangiji.Za su mai da waɗanda suka kama su su zama kamammusu kuma yi mulki a kan waɗanda suka taɓa danne su.3A ranar da Ubangiji ya hutashe ku daga wahala da azaba da muguwar bauta,4za ku yi wa sarkin Babilon wannan ba’a.Mai danniya ya zo ga ƙarshe!Dubi yadda fushinsa ya ƙare!5Ubangiji ya karye sandar mugaye,sandan mulkin masu mulki,6wanda cikin fushi ya kashe mutaneda bugu marar ƙarewa,kuma cikin fushi ya mamaye al’ummaida fushi ba ƙaƙƙautawa.7Dukan ƙasashe suna hutawa suna kuma cikin salama;sun ɓarke da waƙa.8Har itatuwan fir ma da kuma al’ul na Lebanonsuna murna a kanka suna cewa,“Yanzu da aka ƙasƙantar da kai,babu wani mai yankan katakon da ya zo yă yanka mu.”9Kabari a ƙarƙashi duk ya shiryadon yă sadu da kai a zuwanka;yana tā da ruhohin da suka rasu don su gaishe ka,dukan waɗanda sun taɓa zama shugabanni a duniya;ya sa suka tashi daga kujerun sarauta,dukan waɗanda suke sarakuna a kan al’ummai.10Duk za su amsa,za su ce maka,“Ashe kai ma raunana ne, kamar mu;ka zama kamar mu.”11An yi ƙasa da dukan alfarmarka zuwa kabari,tare da surutan garayunka;tsutsotsi sun bazu a ƙarƙashinkatsutsotsi kuma suka rufe ka.12Yaya aka yi ka fāɗo daga samaYa tauraron safiya, ɗan hasken asuba!An fyaɗa ka da ƙasa,kai da ka taɓa ƙasƙantar da al’ummai!13Ka yi tunani a ranka ka ce,“Zan hau zuwa sama;zan ɗaga kursiyinasama da taurarin Allah;zan zauna a kursiyi a kan dutsen taro,a can ƙurewar saman dutse mai tsarki.14Zan haura can bisa gizagizai;zan mai da kaina kamar Mafi Ɗaukaka.”15Amma ga shi an gangara da kai zuwa kabari,zuwa zurfafan rami.16Waɗanda suka gan ka sun zura maka ido,suna tunani abin da zai same ka.“Wannan mutumin ne ya girgiza duniyaya kuma sa mulkoki suka razana,17mutumin da ya mai da duniya ta zama hamada,wanda ya tumɓuke biranentabai kuma bar kamammunsa suka tafi ba?”18Dukan sarakunan duniya suna kwance a mace,kowa a kabarinsa.19Amma an jefar da kabarinkakamar reshen da aka ƙi;an rufe ka da waɗanda aka kashe,tare da waɗanda aka soke da takobi,waɗanda suka gangara zuwa duwatsun rami.Kamar gawar da aka tattake da ƙafa,20ba za a haɗa ka tare da su a jana’iza ba,gama ka hallaka ƙasarkaka kuma kashe mutanenka.Ba za a ƙara ambacizuriyarka masu aikata mugunta ba.21A shirya wuri don a yayyanka ’ya’yansa mazasaboda zunuban kakanninsu;kada a reno su su gāji ƙasarsu cika duniya da biranensu.22“Zan yi gāba da su,”in ji Ubangiji Maɗaukaki.“Zan kau da sunan Babilon da waɗanda suka rage da rai a cikinta,’ya’yanta da zuriyarta,”in ji Ubangiji.23“Zan mai da ita wuri domin mujiyoyida kuma fadama;zan share ta da tsintsiyar hallaka,”Ni Ubangiji Maɗaukaki na faɗa.