Ishaya12hau_bib

Waƙoƙin yabo

1A wannan rana za ku ce,“Zan yabe ka, ya Ubangiji.Ko da yake a dā ka yi fushi da ni,amma yanzu ka daina fushi da nika kuwa ta’azantar da ni.2Tabbatacce Allah shi ne mai cetona;zan dogara gare shi ba kuwa zan ji tsoro ba.Ubangiji, Ubangiji, ne ƙarfina da waƙata;ya zama mai cetona.”3Da farin ciki zan ɗebo ruwadaga rijiyoyin ceto.4A wannan rana za ku ce,“Yi godiya ga Ubangiji, ku kira bisa sunansa;a sanar da wannan abin da ya aikata a cikin al’ummai,a kuma yi shela cewa sunansa mai girma ne.5Ku rera ga Ubangiji, gama ya aikata manyan abubuwa;bari a sanar da wannan ga dukan duniya.6Ku tā da murya ku kuma rera don farin ciki, ya ku mutanen Sihiyona,gama Mai Tsarki na Isra’ila da girma yake a cikinku.”