Ishaya10hau_bib
1Kaiton waɗanda suke kafa dokokin rashin gaskiya,waɗanda suke ba da ƙa’idodin danniya,2don su hana matalauta hakkinsusu kuma ƙi yin shari’ar gaskiya a kan waɗanda suke zaluntar mutanena,suna ƙwace wa gwauraye dukiyarsusuna kuma yi wa marayu ƙwace.3Me za ku yi a ranan nan ta hukunci,sa’ad da masifa ta zo daga nesa?Ga wa za ku tafi don neman taimako?Ina za ku bar dukiyarku?4Babu abin da zai rage sai cizon haƙora a cikin kamammuko mutuwa cikin waɗanda aka kashe.Duk da haka, fushinsa bai huce ba,hannunsa har yanzu yana a miƙe.