Hosiya9hau_bib

Hukunci domin Isra’ila

1Kada ku yi farin ciki, ya Isra’ila;kada ku yi murna kamar waɗansu al’ummai.Gama kun yi rashin aminci ga Allahnku;kuna son hakkokin karuwaa kowace masussuka.2Masussukai da wuraren matsin inabi ba za su ciyar da mutane ba;sabon ruwan inabi zai kāsa musu.3Ba za su ci gaba da zama a ƙasar Ubangiji ba;Efraim zai koma Masaryă kuma ci abinci marar tsarki a Assuriya.4Ba za su zuba hadayun ruwan inabi ga Ubangiji ba,ba kuwa hadayunsu za su gamshe shi ba.Irin hadayun nan za su zama musu kamar burodin masu makoki;duk wanda ya ci su zai ƙazantu.Wannan abincin zai zama na kansu ne;ba zai zo cikin haikalin Ubangiji ba.
5Me za ku yi a ƙayyadaddiyar ranar bukukkuwarku,a ranakun bikin Ubangiji?6Ko da sun kuɓuta daga hallaka,Masar za tă tattara su,Memfis kuma za tă binne su.Sarƙaƙƙiya za tă mamaye kayan azurfansu,ƙayayyuwa su tsiro a cikin tentunansu.7Kwanakin hukunci suna zuwa,kwanakin ba da lissafi suna a kusa.Bari Isra’ila su san da wannan.Saboda zunubanku sun yi yawaƙiyayyarku kuma ta yi yawa,har ake ɗauka annabi wawa ne,mutumin da aka iza kuwa mahaukaci.8Annabi, tare da Allahna,su ne masu tsaro a bisa Efraim,duk da haka tarko na jiransa a dukan hanyoyi,da kuma ƙiyayya a cikin gidan Allahnsa.9Sun nutse da zurfi cikin lalaci,kamar a kwanakin Gibeya.Allah zai tuna da muguntarsuyă kuma hukunta su saboda zunubansu.
10“Sa’ad da na sami Isra’ila,ya zama kamar samun inabi a hamada;sa’ad da na ga kakanninku,ya zama kamar ganin ’ya’yan itace na farko a itacen ɓaure.Amma sa’ad da suka zo Ba’al-Feyor,suka keɓe kansu wa gumaka bankunyasai suka zama abubuwan banƙyama kamar abubuwan da suke ƙauna.11Darajar Efraim za tă yi firiya tă tafi kamar tsuntsu,ba haihuwa, ba juna biyu, ba ɗaukar ciki.12Ko da sun yi renon ’ya’ya,zan sa su yi baƙin cikin kowannensu.Kaitonsusa’ad da na juya musu baya!13Na ga Efraim, kamar birnin Taya,da aka kafa a wuri mai daɗi.Amma Efraim zai fitarda ’ya’yansu ga masu yanka.”
14Ka ba su, ya UbangijiMe za ka ba su?Ka ba su mahaifar da za su yi ɓarin cikida busassun nono.
15“Saboda dukan muguntarsu a Gilgal,na ƙi su a can.Saboda ayyukansu na zunubi,zan kore su daga gidana.Ba zan ƙara ƙaunace su ba;dukan shugabanninsu ’yan tawaye ne.16An ka da Efraim,saiwarsu ta bushe,ba sa ba da amfani.Ko da sun haifi ’ya’yazan kashe waɗanda suka fi ƙauna.”
17Allahna zai ƙi susaboda ba su yi masa biyayya ba;za su zama masu yawo a cikin al’ummai.