1Ku dawo, ya Isra’ila, ga Ubangiji Allahnku.Zunubanku ne sun zama sanadin fāɗuwarku!2Ku ɗauki magana tare da kuku komo wurin Ubangiji.Ku ce masa,“Ka gafarta mana dukan zunubanmuka kuma karɓe mu da alheri,don mu iya yabe ka da leɓunanmu.3Assuriya ba za su iya cece mu ba;ba za mu hau dawakan yaƙi ba.Ba za mu ƙara ce, ‘Allolinmu’wa abin da hannuwanmu suka yi ba,gama a gare ka ne maraya yakan sami jinƙai.”4“Zan gyara ɓatancinsuin kuma ƙaunace su a sake,gama fushina ya juya daga gare su.5Zan zama kamar raɓa ga Isra’ilazai yi fure kamar lili.Kamar al’ul na Lebanonzai sa saiwarsa zuwa ƙasa;6tohonsa za su yi girma.Darajarsa za tă zama kamar itacen zaitun,ƙanshinsa kamar al’ul na Lebanon.7Mutane za su sāke zauna a inuwarsa.Zai haɓaka kamar ƙwayar hatsi.Zai yi fure kamar kuringa,zai zama sananne kamar ruwan inabi daga Lebanon.8Efraim zai ce, me kuma zai haɗa ni da gumaka?Zan amsa masa in kuma lura da shi.Ni kamar koren itacen fir ne;amincinka yana fitowa daga gare ni ne.”9Wane ne yake da hikima? Zai gane waɗannan abubuwa.Hanyoyin Ubangiji daidai ne;masu adalci sukan yi tafiya a kansu,amma ’yan tawaye sukan yi tuntuɓe a kansu.