Ibraniyawa5hau_bib
1Akan zaɓi kowane babban firist daga cikin mutane ne, akan kuma naɗa shi domin yă wakilce su a kan al’amuran Allah, domin yă miƙa kyautai da hadayu saboda zunubai.2Da yake babban firist ɗin mai kāsawa ne, yana iya bin da jahilai da kuma waɗanda suka kauce hanya, a hankali.3Shi ya sa dole yă miƙa hadayu domin zunubansa, da kuma domin zunuban mutane.4Ba wanda yakan kai kansa a wannan matsayi mai girma; sai ko Allah ya kira shi, kamar yadda aka yi wa Haruna.5Haka ma Kiristi bai kai kansa neman ɗaukaka na zama babban firist ba. Allah ne dai ya ce masa,“Kai Ɗana ne;yau na zama Uba a gare ka.”6Ya kuma ya ce a wani wuri,“Kai firist ne na har abada,bisa ga tsarin Melkizedek.”7A lokacin da Yesu ya yi rayuwa a duniya, ya yi addu’o’i da roƙe-roƙe tare da kuka mai zafi da kuma hawaye ga wannan wanda yake da ikon cetonsa daga mutuwa, aka kuwa ji shi saboda tsananin bangirman da ya yi.8Ko da yake shi ɗa ne, ya yi biyayya ta wurin shan wahala9kuma da aka mai da shi cikakke, sai ya zama hanyar samun madawwamin ceto ga dukan waɗanda suke masa biyayya.10Allah kuwa ya naɗa shi yă zama babban firist, bisa ga tsarin Melkizedek.