Ezra6hau_bib
Umarnin Dariyus
1Sarki Dariyus kuwa ya ba da umarni a bincika a duba cikin littattafan tarihin da suke a ajiye a wurin ajiyarsu a Babilon.2Sai aka sami takarda a Ekbatana a yankin Mediya, ga kuma abin da yake rubuce a ciki. Abin tunawa.3A shekara ta farko ta mulkin sarki Sairus, sarki ya ba da umarni game da haikalin Allah a Urushalima, ya ce,Bari a sāke gina haikalin yă zama wurin miƙa hadayu, a kuma aza harsashin ginin haikalin. Tsayinsa zai zama ƙafa tasa’in, fāɗinsa kuma kamu tasa’in.4Za a jera manyan duwatsu jeri uku, da jeri ɗaya na katako. Daga asusun sarki kuma za a biya kuɗin aikin.5Kwanonin zinariya da na azurfan gidan Allah waɗanda Nebukadnezzar ya kwashe daga haikali a Urushalima ya kawo Babilon, a mayar da su wurinsu a haikali a Urushalima; a sa su cikin gidan Allah.6Saboda haka Tattenai, gwamnan Kewayen Kogin Yuferites, da Shetar-Bozenai, da ku masu muƙami na yankin, ku bar wurin.7Kada ku hana wannan aiki na haikalin Allah. Bari gwamnan Yahudawa, da dattawan Yahudawa su sāke gina wannan gidan Allah a wurin da yake a dā.8Na kuma ba da umarni game da abin da za ku yi wa dattawan Yahudawa cikin aikin ginin wannan gidan Allah. Daga asusun sarki a kuɗin da yake shigo wa Kewayen Kogin Yuferites za a biya mutanen nan duka, domin kada aikin yă tsaya.9A tanada musu duk abin da suke bukata. A ba su ’yan bijimai, da raguna, da ’yan tumaki domin miƙa hadaya ta ƙonawa ga Allah na sama, haka kuma dole a tanada wa firistoci alkama, da gishiri, da ruwan inabi, da mai, kullum ba fasawa yadda firistoci suke yi a Urushalima10domin su miƙa hadayu masu daɗi ga Allah na Sama, su kuma yi addu’a domin lafiyar sarki da ’ya’yansa.11Na kuma yi umarni cewa duk wanda ya karya wannan doka sai a fitar da itace daga cikin gidansa, a fiƙe kan itacen, a tsire mutumin, sa’an nan a mai da gidansa juji.12Bari Allah yă sa sunansa yă kasance, yă hamɓarar da duka wani sarki ko mutanen da za su sa hannu don a sāke wannan doka, ko kuma don su rushe haikalin nan a Urushalima. Ni Dariyus na ba da wannan umarni, bari a yi biyayya babu wasa.