Ezra2hau_bib

Waɗanda suka dawo daga bauta

1Ga lissafin waɗanda suka dawo daga bauta a Babilon, waɗanda Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kwasa zuwa bauta a ƙasar Babilon (sun dawo Urushalima da Yahuda, kowa ya koma garinsu.2Sun komo tare da Zerubbabel, da Yeshuwa, da Nehemiya, da Serahiya, da Re’elaya, da Mordekai, da Bilshan, da Misfar, da Bigwai, da Rehum, da Ba’ana).
Ga jerin mazan mutanen Isra’ila.
3Zuriyar Farosh mutum 2,1724ta Shefatiya 3725ta Ara 7756ta Fahat-Mowab (ta wurin Yeshuwa da Yowab) 2,8127ta Elam 1,2548ta Zattu 9459ta Zakkai 76010ta Bani 64211ta Bebai 62312ta Azgad 1,22213ta Adonikam 66614ta Bigwai 2,05615ta Adin 45416ta Ater (ta wurin Hezekiya) 9817ta Bezai 32318ta Yora 11219ta Hashum 22320ta Gibbar 95.21Mutanen Betlehem 12322na Netofa 5623na Anatot 12824na Azmawet 4225na Kiriyat Yeyarim,da Kefira Beyerot 74326na Rama da Geba 62127na Mikmash 12228na Betel da Ai 22329na Nebo 5230na Magbish 15631na ɗayan Elam ɗin 1,25432na Harim 32033na Lod, da Hadid da Ono 72534na Yeriko 34535na Sena’a 3,630.
36Firistoci. Zuriyar Yedahiya (ta wurin iyalin Yeshuwa) 97337ta Immer 1,05238ta Fashhur 1,24739ta Harim 1,017.
40Lawiyawa. Lawiyawa na zuriyar Yeshuwa da Kadmiyel (ta wurin Hodawiya) mutum 74.
41Mawaƙa. Zuriyar Asaf mutum 128.
42Masu tsaron haikali. Zuriyar Shallum, Ater, Talmon, Akkub, Hatita, da Shobai mutum 139.
43Ma’aikatan haikali. Zuriyar Ziha, Hasufa, Tabbawot,44Keros, Siyaha, Fadon,45Lebana, Hagaba, Akkub,46Hagab, Shamlai, Hanan,47Giddel, Gahar, Reyahiya,48Rezin, Nekoda, Gazzam,49Uzza, Faseya, Besai,50Asna, Meyunawa, Nefussiyawa,51Bakbuk, Hakufa, Harhur,52Bazlut, Mehida, Harsha,53Barkos, Sisera, Tema,54Neziya da Hatifa.55Zuriyar bayin Solomon. Zuriyar Sotai, Hassoferet, Feruda,56Ya’ala, Darkon, Giddel,57Shefatiya, Hattil, Fokeret-Hazzebayim, da Ami.58Dukan zuriyar ma’aikatan haikali, da kuma bayin Solomon 392.
59Waɗannan mutanen ne suka zo daga garuruwan Tel-Mela, Tel-Harsha, Kerub, Addan da Immer, amma ba su iya nuna ainihin tushensu daga Isra’ila ba.60’Yan zuriyar Delahiya, Tobiya, da Nekoda 652.
61Daga cikin firistoci kuma, zuriyar Hobahiya, Hakkoz da Barzillai (wanda ya auri diyar Barzillai mutumin Gileyad da ake kuma kira da wannan suna).62Waɗannan sun nemi sunayen iyalansu a cikin littafin da ake rubuta sunayen amma ba su ga sunayensu ba, saboda haka sai aka hana su zama firistoci domin an ɗauka su marasa tsabta ne.63Gwamna ya umarce su cewa kada su ci wani abinci mai tsarki sai firist ya yi shawara ta wurin Urim da Tummim tukuna.
64Yawan jama’ar duka ya kai mutum 42,360,65ban da bayinsu maza da mata 7,337; suna kuma da mawaƙa maza da mata 200.66Suna da dawakai guda 736, alfadarai 245,67raƙuma 435, da jakuna 6,720.
68Sa’ad da suka isa haikalin Ubangiji a Urushalima, sai waɗansu shugabannin iyalai suka yi bayarwar yardar rai ta gudummawarsu domin sāke gina gidan Allah a wurin da yake.69Bisa ga ƙarfinsu suka bayar da darik 61,000 na zinariya, da maina 5,000 na azurfa, da rigunan firistoci guda 100.70Firistoci, da Lawiyawa, da mawaƙa, da masu tsaron ƙofofi, da masu aiki a haikali, tare da waɗansu mutane, da dukan sauran Isra’ilawa suka zauna a garuruwansu.