Ezekiyel27hau_bib

Makoki domin Taya

1Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,2“Ɗan mutum, ka yi makoki domin Taya.3Ka ce wa Taya, wadda take zaune a hanyar shiga zuwa teku, kasuwar masu yawa mutane a bakin teku, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa,“ ‘Kin ce, ya Taya,“Ni kyakkyawa ce cikakkiya.”4Manyan tekuna ne wurin zamanki;maginanki sun sa kyanki ya zama cikakke.5Sun yi dukan katakankidaga itatuwan fir daga Senir;sun kwaso itatuwan al’ul daga Lebanondon su yi miki jigon jirgin ruwa.6Da oak daga Bashansuka yi sandunan tuƙan jirgin ruwada itatuwan kasharina daga bakin tekun Saifurussuka yi daɓe jirgin ruwanki, suka kuma manne masa hauren giwa.7Lilin mai kyau mai ado daga Masar ne filafilan jirgin ruwankisuka kuma zama tutarki;an yi tutarki da shuɗi da shunayyadaga bakin tekun Elisha.8Mutanen Sidon da Arfad su ne matuƙan jirgin ruwanki;gwanayenki, ya Taya, suna ciki a matsayi matuƙan jiragen ruwa.9Masu hikima na Gebal suna cikia matsayin masu tattoshe mahaɗan katakon jirginki.Dukan jiragen ruwa da matuƙansusukan zo wurinki don kasuwanci.
10“ ‘Mutanen Farisa, Lidiya da Futsu ne suka zama sojoji a cikin mayaƙanki.Sun rataye garkuwoyinsu da hulunan kwano a katangarki,suna kawo miki daraja.11Mutanen Arfad da Heleksun yi tsaron katangar a kowace gefe;mutanen Gammadsu ne a hasumiyoyinki.Sun rataye garkuwoyinsu kewaye da katangarki;sun sa kyanki ya zama cikakke.12“ ‘Tarshish ta yi ciniki da ke saboda yawan wadatar kayayyakinki; sun sayi kayan cinikinki da azurfa, ƙarfe, kuza da dalma.13“ ‘Girka, Tubal da Meshek sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki suka biya da bayi da kuma abubuwan da aka yi da tagulla.14“ ‘Mutanen Bet Togarma sun sayi kayan cinikinki da dawakai, dawakan yaƙi da alfadarai.15“ ‘Mutanen Dedan sun yi kasuwanci da ke, bakin teku masu yawa abokan cinikinki ne; sun biya ki da hauren giwa da katakon kanya.16“ ‘Mutanen Aramsun yi ciniki da ke saboda yawan kayanki; suka sayi kayan cinikinki da zumurrudu, da shunayya, da kayan ado, da lilin mai taushi, da murjani, da yakutu.17“ ‘Yahuda da Isra’ila sun yi kasuwanci da ke; sun sayi kayanki da alkama da Minnit da alawa,da zuma, da mai, da ganyaye masu ƙanshi.18“ ‘Mutanen Damaskus sun ga abin da za ki iya bayarwa sai suka yi ciniki da ke, ta sayi kayanki da ruwan inabi daga Helbon, da ulu daga Zahar.19Wedan da Yaban kusa da Uzal, suka sayi kayanki; wato gyararren ƙarfe da kayan yaji.20“ ‘Mutanen Dedan sun sayi kayanki da sirdin zama a kan dawakai.21“ ‘Mutanen Arabiya da dukan sarakunan Kedar abokan cinikinki ne; sun yi ciniki da ke suka sayi kayanki da ’yan raguna, da raguna, da awaki.22“ ‘’Yan kasuwan Sheba da Ra’ama sun yi ciniki da ke; suka sayi kayanki da kayan yaji mafi kyau iri-iri, da duwatsu masu daraja iri-iri, da zinariya.23“ ‘Haran, Kanne da Eden da kuma ’yan kasuwan Sheba, Assuriya da Kilmad sun yi ciniki da ke.24A kasuwarki sun yi ciniki da ke suka sayar miki tufafi masu tsada, da na shuɗi, da masu ado, da dardumai masu ƙyalƙyali da kirtani, da igiyoyi waɗanda aka tuƙa da kyau.25“ ‘Jiragen ruwan Tarshish sun zamamasu jigilar kayanki.Kin cika da kaya masu nauyia tsakiyar teku.26Matuƙan jiragenki sun kai kican cikin manyan tekuna.Amma iskar gabas za tă farfasa ki kucu-kucua tsakiyar teku.27Dukiyarki, cinikinki da kayan kasuwarki,ma’aikatanki na jirgi, matuƙan jiragenki da masu tattoshe mahaɗan katakan jiragenki,’yan kasuwarki da dukan sojojinki,da kuma kowa da yake cikin jirgizai nutsa a tsakiyar tekua ranar da jirginki zai nutse.28Ƙasashen bakin teku za su girgizasa’ad da matuƙan jirginki suka yi kuka.29Dukan waɗanda suke riƙe da matuƙiza su ƙyale jiragensu;ma’aikatan jirage da dukan matuƙan jirageza su tsaya a bakin teku.30Za su tā da muryarsusu yi kuka mai zafi a kanki;za su yayyafa ƙura a kawunansu,su yi ta birgima a cikin toka.31Za su aske kawunansu saboda keza su kuma sa tufafin makoki.Za su yi kuka dominki su yi ɓacin raida kuma kuka mai zafi.32Yayinda suke kuka a kanki kuwa,za su yi makoki dominki suna cewa,“Wa ya taɓa yin shiru kamar Taya,kewaye da teku?”33Sa’ad da kayan cinikinki suka tafi ƙasashen hayi,kin gamsar da al’ummai masu yawa;da dukiyarki masu yawa da kuma kayan cinikinkikin azurtar da sarakunan duniya.34Yanzu teku ta farfashe kicikin zurfafan ruwaye;kayan cinikinki da dukan kamfaninkisun nutse tare da ke.35Dukan mazaunan bakin tekusun giggice saboda masifarki;sarakunansu sun tsorata ƙwaraifuskokinsu kuwa sun yamutse don tsoro.36’Yan kasuwa a cikin al’ummai suna yin miki tsaki;kin zo ga mummunar ƙarsheba za ki ƙara kasancewa ba har abada.’ ”