Mai Hadishi12hau_bib
1Ka tuna da Mahaliccinkaa kwanakin ƙuruciyarka,kafin lokacin wahala ta zoshekaru kuma su ƙarato sa’ad da za ka ce,“Ba na jin daɗinsu,”2kafin rana da haskewata da taurari su daina haske,gizagizai kuma su tattaru bayan da suka sheƙa ruwa;3sa’ad da masu tsaron gida suke rawar jiki,majiya ƙarfi kuma suka rasa ƙarfi,sa’ad da masu niƙa suka daina don ba su da yawa,idanun da suke duba ta taga suka duhunta;4sa’ad da aka rufe ƙofofin shiga titunaƙarar niƙa kuma ya tsagaita;sa’ad da kukan tsuntsaye ta farkar da mutane,ba a kuwa jin waƙoƙinsu,5sa’ad da mutane suke jin tsoron tududa kuma hatsarori a tituna;sa’ad da itacen almon ya toho,fāra kuma ya yi ta jan jikinsa da ƙyar,sha’awace-sha’awace sun kafe.Daga nan mutum ya tafi madawwamiyar gidansaya bar masu makoki suna ta yi.6Ka tuna da shi, kafin igiyar azurfa ta katse,ko tasar zinariya ta fashe;kafin tulu yă ragargaje a maɓulɓula,ko guga ta tsinke a rijiya,7turɓaya ta koma ƙasar da ta fito,rai kuma yă koma ga Allah wanda ya ba da shi.8“Ba amfani! Ba amfani!” In ji Malami,“Gaba ɗaya ba amfani!”