Amos6hau_bib

Kaito ga zaman sakewa

1Taku ta ƙare, ku da kuke zaman sakewa a Sihiyona,da ku waɗanda kuke ji zama a Dutsen Samariya lafiya ne,ku manyan mutanen ƙasar da take sananniya,waɗanda mutanen Isra’ila suke zuwa!2Ku je Kalne ku dube ta;ku wuce daga can zuwa Hamat-rabba,sa’an nan ku gangara zuwa Gat a Filistiya.Sun fi masarautunku biyu ne?Ƙasarsu ta fi taku girma?3Kuna ƙoƙari ku kauce wa wannan muguwar ranakuna kuma jawo mulkin tashin hankali kusa.4Kuna kwanciya a kan gadajen da aka yi musu shimfiɗar hauren giwakuna mimmiƙe a kan kujerunku.Kuna cin naman ƙibabbun ragunada na ƙosassun ’yan maruƙa.5Kuna kaɗa molayenku yadda Dawuda ya yikuna ƙirƙiro waƙoƙi a kan kayan kaɗe-kaɗe.6Da manyan kwanoni kuke shan ruwan inabikuna kuma shafa mai mafi kyau,amma ba kwa baƙin ciki game da kangon da Yusuf ya zama.7Saboda haka za ku zama na farkon da za su tafi zaman bauta;bukukkuwanku da shagulgulanku za su ƙare.

Ubangiji yana ƙyamar girmankan Isra’ila

8Ubangiji Mai Iko Duka da kansa ya rantse, Ubangiji Allah Maɗaukaki ya furta,“Ina ƙyamar girman kan Yaƙub,ba na kuma son kagarunsa;zan ba da birninda duk abin da yake cikinta.”9Ko da mutum goma ne suka ragu a gida guda, su ma za su mutu.10In kuma wani dangi ya shiga don yă fitar da gawawwakin yă ƙone ya kuwa tambayi wani wanda yake ɓoye a can, yana cewa, “Akwai wani tare da kai?” Ya kuwa ce, “Babu,” sai yă ce, “Kul! Kada mu ambaci sunan Ubangiji.”11Gama Ubangiji ya ba da umarni,zai kuma ragargaza babban gidan nan kucu-kucuƙaramin gidan kuwa zai yi rugu-rugu da shi.
12Dawakai sukan yi gudu a kan duwatsu?Wani yana iya yin noma a teku da shanun noma?Amma ga shi kun mai da gaskiya ta zama dafiamfanin adalci kuma ya zama ɗaci,13ku da kuke murna saboda an ci Lo Debar da yaƙikuka kuma ce, “Ba da ƙarfinmu ne muka ƙwace Karnayim ba?”
14Gama Ubangiji Allah Maɗaukaki ya ce,“Zan sa wata ƙasa ta tayar muku, ya ku gidan Isra’ila,wadda za tă matsa muku tundaga Lebo Hamat zuwa kwarin Araba.”