Amos1hau_bib

1Kalmomin Amos, ɗaya daga cikin makiyayan Tekowa, abubuwan da ya gani game da Isra’ila shekaru biyu kafin a yi girgizar ƙasa, a lokacin da Uzziya yake sarkin Yahuda, Yerobowam ɗan Yowash kuma yake sarkin Isra’ila.
2Ya ce,“Ubangiji ya yi ruri daga Sihiyonaya kuma yi tsawa daga Urushalima;wuraren kiwo duk sun bushe,dutsen Karmel kuma ya yi yaushi.”

Hukunci a kan maƙwabtan Isra’ila

3Ga abin da Ubangiji ya ce,“Saboda zunubai uku na Damaskus,har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.Domin sun ci zalunci Gileyadzalunci mai tsanani,4zan sa wuta a gidan Hazayel,da za tă ƙona kagarun Ben-Hadad.5Zan kakkarye ƙofofin Bet-Damaskus;zan hallaka sarkin da yake cikin Kwarin Awenda kuma mai riƙe da sandar mulkin Bet-Eden.Mutanen Aram za su je bauta a ƙasar Kir,”in ji Ubangiji.6Ga abin da Ubangiji ya ce,“Saboda zunubai uku na Gaza,har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.Don sun kwashe al’umma gaba ɗayasun sayar wa Edom,7Zan aika da wuta a katangar Gazata ƙone duk kagarunta.8Zan hallaka sarkin Ashdodda kuma mai riƙe da sandar mulki na Ashkelon.Zan hukunta Ekron,har sai dukan Filistiyawa sun mutu,”in ji Ubangiji Mai Iko Duka.9Ga abin da Ubangiji ya ce,“Saboda zunubai uku na Taya,har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba.Don sun kwashe al’umma gaba ɗaya sun kai su bauta a Edom,ba su kula da yarjejjeniyar da aka yi ta zama kamar ’yan’uwa ba,10zan aika da wuta a Taya,da za tă ƙone kagarunta.”11Ga abin da Ubangiji ya ce,“Saboda zunubai uku na Edom,har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba.Don ya fafari ɗan’uwansa da takobi,babu tausayi,domin ya ci gaba da fusatabai yarda yă huce daga fushinsa ba.12Zan aika wuta a Temanda za tă ƙone kagarun Bozra.”13Ga abin da Ubangiji ya ce,“Saboda zunubai uku na Ammon,har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta shi ba.Don ya tsaga cikin matan Gileyad masu juna biyudon kawai yă ƙwace ƙasar.14Zan sa wuta a katangar Rabbada za tă ƙone kagaruntaza a yi kururuwa a ranar yaƙi,faɗan kuwa zai yi rugugi kamar hadiri.15Sarkinta zai je bauta,shi da ma’aikatansa,”in ji Ubangiji.