2 Sama’ila3hau_bib
1Aka daɗe ana yaƙi tsakanin gidan Shawulu da gidan Dawuda. Dawuda kuwa ya yi ta ƙara ƙarfi, yayinda gidan Shawulu ya yi ta raguwa a ƙarfi.2An haifa wa Dawuda ’ya’ya maza a Hebron.
Ɗansa na fari shi ne Amnon, ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel;3na biyu shi ne Kileyab, ɗan Abigiyel gwauruwar Nabal mutumin Karmel; na uku shi ne Absalom, ɗan Ma’aka ’yar Talmai sarkin Geshur;4na huɗu shi ne Adoniya, ɗan Haggit; na biyar shi ne Shefatiya, ɗan Abital;5na shida kuma shi ne Itireyam, ɗan Egla matar Dawuda.
An haifi waɗannan wa Dawuda a Hebron.