1 Sarakuna4hau_bib
Shugabanni da gwamnonin Solomon
1Sai Sarki Solomon ya yi mulki a bisa dukan Isra’ila.2Waɗannan su ne manyan shugabanninsa.Azariya ɗan Zadok shi ne firist;3Elihoref da Ahiya, ’ya’yan Shisha maza, su ne marubuta. Yehoshafat ɗan Ahilud, shi ne mai lura da takardu.4Benahiya ɗan Yehohiyada, shi ne shugaban mayaƙa. Zadok da Abiyatar, su ne firistoci.5Azariya ɗan Natan, shi ne mai lura da shugabannin yanki. Zabud ɗan Natan, shi ne firist da kuma mai wa sarki shawara.6Ahishar, shi ne sarkin fada. Adoniram ɗan Abda, shi ne mai lura da aikin gandu.7Solomon yana da gwamnoni yankuna goma sha biyu a bisa dukan Isra’ila, waɗanda suke tanaji abinci domin sarki da kuma gidan sarauta. Kowanne yakan tanada abinci na wata ɗaya a shekara.8Ga sunayensu,
Ben-Hur, shi ne a ƙasar tudun Efraim;9Ben-Deker, shi ne a Makaz, Sha’albim, Bet-Shemesh da Elon Bet-Hanan;10Ben-Hesed, shi ne a Arubbot (Soko da dukan ƙasar Hefer);11Ben-Abinadab, shi ne a Nafot Dor (ya auri Tafat ’yar Solomon);12Ba’ana ɗan Ahilud, shi ne a Ta’anak da Megiddo, da kuma dukan Bet-Sheyan biye da Zaretan ƙasa da Yezireyel, daga Bet-Sheyan zuwa Abel-Mehola a ƙetaren Yokmeyam;13Ben-Geber, shi ne a Ramot Gileyad (Mazaunan Yayir ɗan Manasse a Gileyad suna a ƙarƙashinsa, haka ma yankin Argob a Bashan tare da manyan biranen sittin masu katanga da suke da ƙyamare na tagulla);14Ahinadab ɗan Iddo, shi ne a Mahanayim;15Ahimawaz, shi ne a Naftali (ya auri Basemat ’yar Solomon);16Ba’ana ɗan Hushai, shi ne a Asher da Bayelot;17Yehoshafat ɗan Faruwa, shi ne a Issakar;18Shimeyi ɗan Ela, shi ne a Benyamin;19Geber ɗan Uri, shi ne a Gileyad (ƙasar Sihon sarkin Amoriyawa da kuma Og sarkin Bashan). Shi ne kaɗai gwamna a bisa yankin.