1 Tarihi3hau_bib
’Ya’yan Dawuda maza
1Waɗannan su ne ’ya’yan Dawuda maza da aka haifa masa a Hebron.Ɗan farinsa shi ne Amnon ɗan Ahinowam mutuniyar Yezireyel; na biyun, Daniyel ɗan Abigiyel mutuniyar Karmel;2na ukun, Absalom ɗan Ma’aka ’yar Talmai sarkin Geshur; na huɗun, Adoniya ɗan Haggit;3na biyar, Shefatiya ɗan Abital; da kuma na shida, Itireyam ta wurin matarsa Egla.4Waɗannan su ne aka haifa wa Dawuda a Hebron, inda ya yi mulki shekaru bakwai da wata shida.
Dawuda ya yi mulki a Urushalima shekaru talatin da uku,5kuma waɗannan su ne yaran da aka haifa masa a can.
Shimeya,Shobab, Natan da Solomon. Waɗannan huɗu ne Bat-shuwa’yar Ammiyel ta haifa.6Akwai kuma Ibhar, Elishama, Elifelet,7Noga, Nefeg, Yafiya,8Elishama, Eliyada da Elifelet, su tara ne duka.9Dukan waɗannan ’ya’yan Dawuda ne maza, ban da ’ya’yansa maza ta wurin ƙwarƙwaransa. Tamar ita ce ’yar’uwarsu.