1 Tarihi27hau_bib
Ɓangarorin mayaƙa
1Wannan shi ne jerin Isra’ilawa, kawunan iyalai, shugabannin dubu-dubu da shugabannin ɗari-ɗari, da manyan ma’aikatansu, waɗanda suka yi wa sarki hidima a dukan abin da ya shafi ɓangarorin mayaƙan da suke aiki wata-wata a dukan shekara. Kowane sashe yana da mutane 24,000.2Wanda yake lura da sashe na fari, na wata na farko, shi ne Yashobeyam ɗan Zabdiyel. Akwai mutane 24,000 a sashensa.3Shi zuriyar Ferez ne kuma babba na dukan shugabannin mayaƙa don wata na farko.4Wanda yake lura da sashen don wata na biyu shi ne Dodai mutumin Ahowa; Miklot ne shugaban sashensa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.5Shugaban mayaƙa na uku, don wata na uku, shi ne Benahiya ɗan Yehohiyada firist. Shi ne babba kuma akwai mutane 24,000 a sashensa.6Wannan shi ne Benahiya wanda yake ɗaya daga cikin jarumawa Talatin nan kuma shi ne yake babba a cikin Talatin ɗin. Ɗansa Ammizabad ne yake lura da sashensa.7Na huɗu, don wata na huɗu, shi ne Asahel ɗan’uwan Yowab; ɗansa Zebadiya shi ne magājinsa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.8Na biyar don wata na biyar, shi ne Shamhut mutumin Izhar shugaban mayaƙa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.9Na shida, don wata na shida, shi ne Ira ɗan Ikkesh mutumin Tekowa. Akwai mutane 24,000 a sashensa.10Na Bakwai, don wata na bakwai, shi ne Helez mutumin Felon, mutumin Efraim. Akwai mutane 24,000 a sashensa.11Na takwas, don wata na takwas, shi ne Sibbekai mutumin Husha, mutumin Zera. Akwai mutane 24,000 a sashensa.12Na tara, don wata na tara, shi ne Abiyezer mutumin Anatot, mutumin Benyamin. Akwai mutane 24,000 a sashensa.13Na goma, don wata na goma, shi ne Maharai mutumin Netofa, mutumin Zera. Akwai mutane 24,000 a sashensa.14Na goma sha ɗaya, don wata goma sha ɗaya, shi ne Benahiya mutumin Firaton, mutumin Efraim. Akwai mutane 24,000 a sashensa.15Na goma sha biyu don wata goma sha biyu, shi ne Heldai mutumin Netofa, daga iyalin Otniyel. Akwai mutane 24,000 a sashensa.Manyan shugabannin Kabilu
16Shugabannin da suke bisa kabilan Isra’ila,bisa mutanen Ruben su ne, Eliyezer ɗan Zikri; bisa mutanen Simeyon shi ne, Shefatiya ɗan Ma’aka17bisa mutanen Lawi shi ne, Hashabiya ɗan Kemuwel; bisa mutanen Haruna shi ne, Zadok;18bisa mutanen Yahuda shi ne, Elihu, ɗan’uwan Dawuda; bisa mutanen Issakar shi ne, Omri ɗan Mika’ilu;19bisa mutanen Zebulun shi ne, Ishmahiya ɗan Obadiya; bisa mutanen Naftali shi ne, Yerimot ɗan Azriyel;20bisa mutanen Efraim shi ne, Hosheya ɗan Azaziya; bisa rabin kabilar Manasse shi ne, Yowel ɗan Fedahiya;21bisa ɗayan rabi kabilar Manasse a Gileyad shi ne, Iddo ɗan Zakariya; bisa mutanen Benyamin shi ne, Ya’asiyel ɗan Abner;22bisa mutanen Dan shi ne, Azarel ɗan Yeroham.
Waɗannan su ne shugabanni a bisa kabilan Isra’ila.23Dawuda bai ƙirga mutanen da suke ’yan shekara ashirin ko ƙasa ba, domin Ubangiji ya yi alkawari zai sa Isra’ila su yi yawa kamar taurari a sararin sama.24Yowab ɗan Zeruhiya ya fara ƙirgan mutanen amma bai gama ba. Hasala ta sauko a kan Isra’ila saboda wannan ƙirge, ba a kuma shigar da adadin a littafin tarihin Sarki Dawuda ba.